A daidai lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ke shirin mika ragamar mulki ga Bola Ahmed Tinubu, fagen siyasar Najeriya na ci gaba da daukar zafi musamman game da shari'ar sauraren kararrakin zabe da nade-naden mukamai.
Shugaba Buhari da shugaban jam'iyyar APC a lokacin da yake tallata takarar TinubuHoto: Nigeria Prasidential Villa
Talla
Jam'iyyu biyar da ke kalubalantar nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaben shugaban kasa a watan Fabirairun da ya gabata sun fara bayyana dalilansu a gaban kotun sauraren kararrakin zaben zaben shugaban kasa da gwamnoni da 'yan majalisun tarayya. Wannan na zuwa ne makonni kalilan kafin rantsar da zababbun a karshen watan Mayu.