Siriya ta zargi Isra'ila da jefa kasar cikin yaki
July 17, 2025Jiragen saman Isra'ila sun rika kai hare-hare a sasa daban-daban na kasar Siriya tun a ranar Litinin. Kwatsam a Laraba Isra'ila ta kaddamar da wani mummunan hari kan ma'aikatar tsaron Siriya da ke babban birnin Damascus.
Wadannan jerin hare-haren ne suka sa shugaban kasar ta Siriya Ahmad al-Sharaa yi wa duniya jawabi ta kafar talabijin din kasar da asubahin Alhamis.
Karin Bayani:Isra'ila ta sake aika dakaru zuwa Siriya
al-Sharaa ya zargi Isra'ila da amfani da rashin tabbas da ya biyo bayan sauyin mulki don kai hari kan muhimman ababen more rayuwa inda ya ce Isra'ila na kokarin dakile sake gina Siriya ne.
"Al shara ya ce a yau, yayin da muke fuskantar wannan sabon kalubale, mun tsinci kanmu a cikin fafutukar kare hadin kan kasar mu, mutuncin jama'armu, da jajircewar al'ummarmu. Isra'ila, wadda kullum ke neman dagula zaman lafiyarmu tun bayan faduwar tsohuwar gwamnati, na kokarin sake mayar da kasar mu zuwa filin fitina mara karewa tare da neman kawo rarrabuwar kawunanmu da raunana karfinmu na sake gina kasa".
Shugaban na Siriya ya kara da cewa karfi kadai ba ya tabbatar da nasara, kuma babu wanda ya san inda fitina za ta tsaya idan aka tayar da ita.
Yayin da yake magana kan rikicin cikin gida a lardin Sweida da ake yi da yan kabilar Druze a kudancin kasar kuwa, al-Sharaa ya ce gwamnati ta shiga tsakani ne don kawo karshen fadace-fadace tsakanin kungiyoyin da ke rike da makamai a cikin gida.
Karin Bayani: Dakarun Isra'ila sun ragargaza cibiyar sojojin Siriya
"Ya ce Siriya ba za ta taba zama wuri na rarrabuwar kawuna ko, wargajewa, ko kuma rikicin addini ba. Muna tabbatar da cewa kare hakkoki da 'yancin al'ummar mu yana daga cikin manyan abubuwan da muke bai wa muhimmanci. Mun ki yarda da duk wani yunkuri na cikin gida ko na waje da ke kokarin raba kawunanmu. Mu duka 'yanuwan juna ne a cikin wannan kasa, kuma ba za mu yarda kowace kungiya ta bata kyakkyawar sunan da muke da shi ba".
'Yan Siriya da dama irinsu AHLAM AL-OMAR mai shekara 57 sun yi Allah wadai da wadannan hare-haren na Isra'ila a kan kasarsu, sannan sun bukaci masu fada a ji su tsawatar.
"Tabbas, muna fatan Isra'ila ba za ta sake jefa mana bamabamai ba, kuma babu wanda zai sake kai mana hari ko wani bangare na kasar mu daga ko ina. Muna fatan za mu hadu mu goyi bayan juna, kuma kowa ya amince da juna".
Kasashen duniya irinsu China sun soki hare-haren na Isra'ila a kan Siriya inda mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajenta, Lin Jian ke cewa dole ne a guji duk wani abu da zai iya kara tayar da hankali a Gabas ta Tsakiya a yayin da rikice-rikice ke ci gaba da aukuwa.