SiyasaSiriya
Siriya ta kawo karshen farmaki a Latakia
March 10, 2025Talla
Ministan tsaron Siriya ya sanar da kawo karshen farmakin da suka kaddamar a gabar kogi. Kakakin ma'aikatar tsaron Kanar Hassan Abdel-Ghani ya ce sojojinsu sun murkushe gyauron yan tada kayar bayan a yankunan Latakia da Tartus.
Kungiyar sa ido kan kare hakkin bil Adama a Siriya wadda ke da mazauninta a Burtaniya ta ruwaito cewa an kashe fararen hula 973 a arangama wanda ke zama tarzoma mafi muni cikin fiye da shekaru goma.
Tarzomar ta barke ne bayan da yan bindiga wadanda ke goyon hambararren shugaban kasar Bashar al Assad suka yi wa sojojin Siriya da ke aikin sintiri kwantar bauna, wanda ya kai ga mummunan arangama da kuma kashe kashen ramuwar gayya.