Siriya: Kura ta lafa a Sweida
July 20, 2025Alkalumma sun yi nuni da cewa a kalla mutane 900 suka rasa rayukansu a rikicin da aka kwashe kwanaki ana gwabzawa a lardin na Sweida da ke Siriya. A ranar Asabar ce dai mayakan suka fattaki kungiyoyin da ke gwagwarmaya da makamai, wanda hakan ya samu ne bayan da gwamnatin Siriyar ta amince da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da ta samu goyon bayan Amurka, a wani mataki na hana Isra'ila daukar wani matakin sojin.
Karin bayani:An ayyana tsagaita wuta a rikicin yankin kudancin Siriya
Jim kadan bayan amincewa da yarjejeniyar tsagaita bude wuta, shugaban riko na Siriya, Ahmed al-Shara ya sha alwashin kare yan Druze mabiya mazhabar Shi'a da ke zama tsiraru a kasar. Sai dai kuma Isra'ila ta ce ba ta yi ammana da alkawuran Sharaa ba, tana mai nuni da irin rikicin da tsiraru kamar Alawites da Druze ke fadawa tun lokacin da ya karbi mulki.