Tasirin cire takunkumin Amurka a Siriya
May 14, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya dauki matakin dage takunkumin da aka kakabawa kasar Siriyan ne cikin dare, inda aka yi ta harbe-harben bindigogi domin yin murna. A Aleppo birni na biyu na mafi girma a Siyria, mutane da dama maza da mata da yara ne suka yi dafifi a dandalin Saadallah Al-Jabiri suna rera wake-wake na murna tare da daga sabuwar tutar kasar. Trump ya sanar da cire takunkumin da Amurkan ta kakabawa Siriya ne, a birnin Riyadh na Saudiyya. Takunkumin dai na da matukar tasiri ga tattalin arzikin Siriya, kasar da aka shafe shekaru 14 ana yakin basasa a cikinta. Ganawar Trump da shugaban Siriya na gwamnatin masu tsattsauran ra'ayi Ahmad al-Sharaa ta gudana ne, duk da adawar da Isra'ila da ke zama babbar kawa ga Amurkan ke yi da ganawar tasu.
Shugaban na Amurka ya yi kira ga sabon shugaban Siyrian wanda ya hau kan karagar mulki a watan Disambar da ya gabata bayan hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad da ya amince da yarjejeniyar Abraham, wadda ta sanya kasashen Larabawa da dama suka amince da Isra'ila a matsayin kasa a shekarar ta 2020. Trump ya kuma bukaci Al Sharaa da ya kori mambobin kungiyoyin Falasdinawan da ke dauke da makamai da kuma daukar nauyin gidajen yari da ke hannun 'yan kungiyar IS a Siyria, wanda a halin yanzu dakarun Kurdawa ke da iko da su. Sai dai makwabciyarta Turkiya, na nuna adawa da umarnin. Kasar Syria dai ta kasance karkashin takunkumin kasa da kasa tun shekarar 1979, sai dai an tsaurara shi bayan da gwamnatin Bashar al-Assad ta murkushe zanga-zangar neman dimukuradiyya a shekarar ta 2011. Bayan Amurka dai Tarayyar Turai da Birtaniya da Kanada suma sun sassauta takunkuminsu a kan Siriyan. Baya ga kasar Saudiyya,tuni shugaban na Amurka ya isa makwabciyarta Katar kafin ya karkare ziyarar tasa a yankin Gabas ta Tsakiyar a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.