Shugabannin Turai za su gana da Trump kan Ukraine
August 13, 2025Shugabannin Turai da na Ukraine za su zanta da Shugaban Amurka Donald Trump ta intanet a yau Laraba kafin taronsa da Vladimir Putin na Rasha.
Shugabannin na Turai na kokarin ganin an kare manufofin Ukraine ne tare da nuna hadarin rashin yin hakan a kokarin Amurka na samar da tsagaita wuta tsakanin Rasha da Ukraine.
Trump zai gana da Putin a Amurka
Trump zai karbi bakuncin Putin ne don tattaunawa a birnin Alaska a ranar Juma'a kuma shugaban Amurka ya ce tattaunawar za ta kasance muhimmiya a kokarinsa na kawo karshen yakin Rasha da Ukraine.
Shugaban Amurka ya ce dole Kyiv da Moscow su mika wani bangare na kasashensu domin kawo karshen yakin kuma tuni sojojin Rasha suka riga suka mamaye kusan kashi daya cikin biyar na Ukraine.
EU ta gaza amince da kakaba wa Rasha sabbin takunkumi
Tattaunawar ta yau Laraba za ta kunshi kasashen Jamus da Findland da Faransa da Burtaniya da Italiya da Poland a cewar mai magana da yawun gwamnatin Jamus.