Shugabannin Turai sun yi maraba da shirin tallafa wa Girika
July 22, 2011Shugabannin ƙasashen Turai masu amfani da takardun kuɗin Euro sun amince da wani tallafin gaggawa na biyu ga ƙasar Girika domin ceto ta daga talaucewa. A taron ƙoli na musamman da suka gudanar a birnin Brussels shugabannin sun sanar cewa kungiyar tarayyar Turai EU da Asusun ba da Lamuni na duniya IMF za su ba da Euro miliyan dubu 109 ga sabon shirin tallafin. A karon farko hukumomin kuɗi sun amince su ba da gudunmawar Euro miliyan dubu 37 cikin tsukin shekaru uku. Shugaban majalisar zartaswar EU Herman Van Rompuy ya ce ya kamata a daƙile barazanar daga yaɗuwa a sauran ƙasashen dake amfani da kuɗin Euro.
"Mun yanke muhimman shawarwari guda uku da dukkanmu muka goyawa baya. Mun inganta matsayin Girika na karɓar bashi. Mun ɗauki matakin hana matsalar bazuwa. Sannan a ƙarshe mun ƙuduri aniyar inganta kula da rikicin kuɗi a tsakanin ƙasahen yankin takardun kuɗin Euro."
Ita ma shugabar IMF Christine Lagarde ta yi maraba da shirin tana mai cewa ya kamata a gaggauta aiwatar da matakan.
Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yaba da sabon taimakon kuɗin ga Girika da cewa muhimmin mataki ne da zai tabbatar da makomar Turai. Ta ce ga al'umar Jamus, taimakon na nufin ƙarin tabbaci ga takardun kuɗin bai ɗaya da kuma matsayin rayuwarsu. Ta ce Euro ya wuce takardun kuɗin, yana matsayin wata babbar haɗakar Turai. Saboda haka tallafin ga Girika wani mataki ne kan wannan turba.
"Ba magana ake game da wani gagarumin shirin ceto Girika ba, a'a mun fi mayar da hankali kan shirin maido da ƙasar kan kyakkyawan matsayin da za ta iya yin goggaya."
A nasa ɓangaren shugaban Faransa Nikolas Sarkozy cewa yayi yarjejeniyar da taron ya cimma za ta rage wa Girika nauyin dake kan kasafin kuɗinta.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu