Shugabannin Turai sun amince da yi wa Rasha taron dangi
May 16, 2025Talla
Da yake karin haske kan matsayar tasu ta yi wa Rasha taron dangi, firaministan Birtaniya Keir Starmer ya bayyana cewa sun dauki matakin ne kasancewar kasashen biyu sun gaza cimma yarjejeniyar tsagaita wuta.
Starmer ya bayyana cewa sun dauki wannan matakin ne bayan ganawarsu da shugaban Ukraine da kuma tattaunawar da suka yi da Shugaba Donald Trump na Amurka ta wayar tarho, inda kuma suka amince cewa ba za su lamunci matakan Rasha dangane da batun sulhun ba.
Shugabanin kasashen nahiyar Turan sun hallara ne a birnin na Tirana, a taronsu da Shugaba Volodymyr Zelenskyy na Ukraine ya samu halarta.