Shugabannin Turai na tattauna basukan nahiyar
October 26, 2011Da yammacin laraban nan ce shugabannin Turai suka buɗe taron tattauna matsalolin basussukan turai a birnin Brussels. Shugabannin ƙasashen turai dai na gudanar da wannan taro karo na biyu ne cikin tsukin kwanaki uku. Kasuwannin hada-hadar kuɗi da masana'antu, sun bukaci da a samar da mafita mai ma'ana dangane da matsalolin basussuka da ke addabar nahiyar. Batutuwa da ake nazari akai sun haɗar da karawa bankunan turai kuɗaɗen jari da yafe wa ƙasar Girka ɗumbin basuka da ake binta da inganta shugabanci mai ma'ana kan harkokin tattali tare da kara faɗaɗa gidauniyar ceto. Taron dai zai mayar da hankali kan priministan Italiya Silvio Berlusconi, wanda aka bukace shi komawa taron na Brussels a yau, da tabbataccen tsarin inganta tattalin arziki da rage dumbin bashin da ake bin kasarsa. Berlusconi dai ya tsallake rijiya ta baya dangane da rugujewar gwamnatinsa, tare da cimma yarjejeniyar jami'iyyar da suke haɗaka a gwamnati, dangane da garon bawul wa tsarin biyan kuɗaɗen Pension a Italiya.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Yahouza Sadissou Madobi