Inganta dangantakar Kanada da China
June 6, 2025Firaminista Mark Carney na kasar Kanada a wannan Jumma'a ya tattauna da Firaminista Li Qiang na kasar China, kan hanyoyin da kasashen biyu za su inganta dangantakarsu, wadda ta yi tsami cikin shekarun da suka gabata. Carney ya shaida wa manema labarai cewa kasarsa ta Kanada ta dauki matakan tattaunawa da kuma inganta dangantaka da China. Sai dai bai ce komai ba kan batun kare hakkin dan Adam a China da ke abubuwan da suka haifar da sabanin a baya.
Karin Bayani: Shugaban Amurka ya karbi bakuncin firaministan Kanada
Shi ma Firaminista Narendra Modi na Indiya ya bayyana cewa yana shirin ganwa da takwaransa na Kanada Mark Carney, lokacin taron gaggan kasashe masu arzikin masana'antu na kungiyar G7, wanda aka gayyaci jagoran na Indiya.
Ita dai Indiya ba ta cikin kasashen amma Firaminista Carney na Kanada mai masaukin bakin ya gayyaci takwaransa na Indiya, lokacin da shugabannin biyu suka tattauna ta wayar tarho, da ma hanyoyin da za su inganta dangantaka tsakanin kasashen.