Shugaban Turkiyya Erdogan bai damu da zanga-zangar adawa ba
March 26, 2025Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya ya ce babu wani abu da zai girgiza shi duk da da jerin zanga-zangar adawa da ta mamaye titunan kasar a yanzu, biyo bayan kama babban abokin hamayyarsa magajin garin Santambul Ekrem Imamoglu.
Karin bayani:Ekrem Imamoglu zai tsaya takarar shugaban kasa a Turkiyya
Mr Erdogan na ba da wannan tabbaci ne a yau Laraba, lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban 'yan majalisar dokokin kasar na jam'iyyarsa ta AKP a birnin Ankara.
Karin bayani:Turkiyya ta kama daruruwan masu boren kin jinin gwamnati
A ranar Lahadi kotu ta ba da umarnin ci gaba da tsare Mr Imamoglu don fuskantar tuhumar zargin cin hanci da rashawa, lamarin da ya sake tunzura magoya bayansa fantsama kan titunan kasar suna zanga-zanga, yayin da jami'an tsaro suka cafke mutane sama da dubu daya a cikinsu.