Al-Sharaa na neman amincewar kasashen duniya
February 4, 2025Ziyarar sabon shugaban rikon kwarya na Kasar ta Siriya,Ahmad Al-sharaa zuwa kasashen da yake da alaka ta kut da kut da su,wato Saudiya da Turkiya,wadanda aka yii amanar sun ejiga-jigan da suka taimakamasa da kudi har ya yi nasarar hawa kan karagar mulkin kasar.
Wannan ziyarar dai ta gaisuwa ce da neman iri,kamar shugaban na Siriya Ahmad al-sharaa din ke fadi a yayin ganawarsa da Yarima Muhammad Bin Salman,mai jiran gadon mulkin Saudiya:
''Muna alfahari da ku kan irin taimako da goyan bayan da ku ka ba mu har muka yi nasarar yenta al,ummar Siriya daga mulkin kama karya da babakeren da Iran ta yi a kasarmu.''
A nasa bangaren ,Bin Salman ,wanda kasarsa Saudiya ke cike da murnar yadda Ahmad Al-sharaa ,ya biya mata babban burinta na kawar da babbar abokiyar hamayyarta Iran daga babakeren da ta yi a Siriya na tsawon gwamman shekaru.
Ya sha alwashin tallafa wa sabuwar gwamnatin ta Siriya tsayawa da kafafuwanta dama taimakawa wajen ganin an dage mata tarin takunkuman da aka kakaba mata''
Masharhanta irin su Dr Talal Bandar na cibiyar binciken diplomasiyya ta birnin Riyadh na Saudiya ,sun yi amanar cewa,akwai wata manufa ta daban da ta sanya sabon shugaban na Siriya fara ziyararsa ta ketare daga Saudiya,kan ban da mika kokon barar da yake ga kasar ta Saudiya:
''Ziyarar da Ahmad Al-Sharaa ke yi a Saudiya,kasar da kasashen yamma ke dauka a matsayin kasa mai sassaucin ra,ayin Islama da ake hulda da ita a lamuran duniya,wani sako ne da matashin sabon shugaban na Siriya ke son isarwa duniya kan cewa.
Ya dawo daga rakiyar ra,ayin rikau din da ya kai ga ake jerantashi cikin kasurguman 'yan ta,addan da ake nema a duniya ruwa a jallo.''
Hakazali,zarcewar da Al-Sharaa din ya yi daga Saudiya zuwa Turkiya a matsayin kasa ta biyu da ya ke ziyarta,wani sako ne ga duniya kan koyi da shugaban Turkiyya ,wanda a matsayinsa na mai rajin Islama,ya yi nasarar bunkasa tattalin arzikin kasarsa tare da inganta alaka da kasashen duniya.