Koriya ta Arewa ta yi gwajin sabbin makamai
August 24, 2025Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya jagoranci gwaji wasu sabbin makamai masu linzami da na'urorin kare sararin samaniya a ranar Asabar, a daidai lokacin da Pyongyang ke zargin Koriya ta Kudu da yunkurin tayar da zaune da tsaye a kan iyakarta.
Ko da sike ba a bayar da cikakken bayani dangane da wadannan sabbin makamai ba, amma kamfanin dallancin labaran Koriya ta Arewa KCNA ya ruwaito cewa yanayin aikin makaman da kuma tashinsu cikin gaggawa ya dogara kan wata fasahar zamani ta musamman.
Sanarwar gwajin wadannan sabbin makamai na zuwa ne bayan da sojojin Koriya ta Kudu suka sanar da cewa sun yi harbin gargadi kan takwarorinsu na Koriya ta Arewa da suka tsallaka iyakar kasar a ranar Talata, lamarin da Pyongyang ta bayyana a matsayin tsokanarta fada.