SiyasaAfirka
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Mali ya isa Rasha
June 22, 2025Talla
Shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Mali Janar Assimi Goita ya fara ziyara a kasar Rasha, inda ake sa ran a wannan Litinin (23.06.2025) zai gana da Shugaba Vladimir Putin kamar yadda bayyana suka tabbatar. Ita dai Rasha tana taimakon kasar ta Mali da ke yankin yammacin yaki da kungiyoyin jihadi masu dauke da makamai.
Karin Bayani: Gwamnatin Mali ta tsawaita wa'adin shugabancin Janar Goita
Shi dai Janar Assimi Goita ya jagoranci juyin mulki sau biyu a shekara ta 2020 da kuma 2021, kuma mayakan Rasha suna taimakjon kasar kan tsagerun masu dauke da makamai da ke neman kwace madafun iko. Tun shekara ta 2012 kasar Mali ta fada cikin rikice-rikice na kungiyoyin jihadi da kuma na 'yan awaren na kabilanci.