SiyasaAsiya
Shugaban China ya isa Cambodiya
April 17, 2025Talla
Shugaba Xi Jinping na China ya gana da Firaminista Hun Manet na Cambodiya a matakin karshen na ziyarar kasashe uku na Kudu maso Gabashin Asiya da shjugaban na China yake yi domin bunkasa harkokin kasuwanci da cinikayya tsakanin kasashen.
Karin Bayani: Yakin kasuwanci tsakanin China da Amurka ya fara gadan-gadan
Shugaba Xi ya isa kasar ta Cambodiya bayan ziyarar kasashen Vietnam da Malesiya, yayin da China take kokarin bunkasa kasuwanci da sauran kasashen duniya musamman bayan matakin gwamnatin Amurka na kakaba kufin fito mai yawa kan kayayyaki da China take shigyarwa zuwa Amurka.
Lokacin ziyarar Shugaba Xi Jinping ya ce kasarsa ta China za ta kara yawan kayayyakin amfanin gona da take saya daga Cambodiya.