An rufe rediyon Amurka VOA
March 16, 2025Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanya hannu kan dokar umarnin takaita ayyukan wasu hukumomin kasar guda shida da rushe wasu baki-daya, ciki har da kafar yada labarai ta Voice of America wato VOA.
Karin bayani:Kasashen G20 na cikin fargaba saboda matakan Donald Trump
Sauran hukumomin sun hada da gidajen adana kayan tarihi da dakunan karatu da bangaren kula da marasa galihu da ke kwana kan tituna, har ya nada 'yar jarida Kari Lake a matsayin daraktar hukumar da za ta kula da rushe wadannan hukumomi, wadanda Trump ya zarga da yada labaran nuna masa kiyayya.
Karin bayani:Trump ya sha alwashin karin kaso 50 na haraji kan Kanada
Sama da shekaru tamanin kenan da kafa VOA wadda ke yada shirye-shiyenta cikin harsuna 40, ta rediyo da talabijin da intanet da shafukan zumunta na zamani.