SiyasaArewacin Amurka
Ganawar Amurka da Kanada
May 6, 2025Talla
Shugaba Donald Trump na Amurka ya gana da sabon Firaminista Mark Carney na kasar Kanada a fadar mulkin Amurka na White House, inda tattaunawar kasuwanci kan kufin fito da kuma barazanar mamaye Kanada a mastayi wata jiha ta Amurka suka mamaye zaman shugabannin biyu.
Karin Bayani: Jam'iyyar Liberal za ta ci gaba da mulkin Kanada
Shugaban Amurka yana ganawar da Firaministan Kanada yayin da kasashen ke takun saka kan harkokin kasuwanci bayan Amurka ta kakaba kudin kito kan kayayyakin Kanada yaiyn da ita Kanada ta mayar da martani.
Firaminista Carney na Kanada ya dauki madafun iko tare da lashe zaben kasar lokacin da dangantaka tsakanin kasashen biyu ta yi tsami.