SiyasaAmurka
Donald Trump na shirin cika kwanaki 100 a kan mulki
April 21, 2025Talla
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yana fatan cewar za a cimma yarjejeniyar kawo yaki tsakanin Rasha da Ukraine a cikin wannan makon.
Shugaban ya bayyana haka ne, cikin wani sako da ya wallafa ta kafar sadawar ta Truth Social a daidai lokacin da yake shirin cika kwanaki 100 kan karagar mulki a ranar Ltinin mai zuwa.
Tun farko Donald Trump ya yi alkawarin kawo karshen yakin Ukraine cikin sa'o'i 24. Sai dai kusan kwanaki dari bayan komawarsa fadar White House, babu wani sakamako da ake iya gani.
Daf da kwanakin darin da ke shirin cika, shugaba Trump na ci gaba da shan sukka saboda sauye-sauyen da yake kaddamarwa a Amurkar.