Shugaba Zelensky na Ukraine na kan hanyar zuwa Saudi Arebiya
March 10, 2025Shugaba Volodymyr Zelenskiy na Ukraine na kan hanyarsa ta zuwa Saudi Arebiya don ganawa da Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman, gabanin tattaunawa da wakilan gwamnatin Amurka don lalubo hanyoyin kawo karshen yakin da kasarsa ke gwabzawa da Rasha tsawon shekaru uku.
Saudi Arebiya ta taka rawar samar da masalahar musayar fursunoni tsakanin Rasha da Ukraine a baya, kuma a watan Fabrairun da ya gabata ma ta karbi bakuncin jami'an Rasha da na Amurka da suka yi tataunar fahimtar juna ta daidaita sabanin diflomasiyyar da ke tsakaninsu, sannan kuma suka bude kokar fara tattauna hanyar kawo karshen yakin Ukraine.
Karin bayani:Ukraine ta amince da bukatar cinikin ma'adinai da Amurka
Ganawar shugaba Zelenskiy da jakadun Amurka da za a yi, ita ce ta farko tun bayan tashi baran-baran da ya yi da shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House a farkon wannan wata.
Mr Trump ya zargi Zelenskiy da jan kafa wajen ganin an kawo karshen yakin.