Shugaba Zelenky ya gana da shugabannin Indiya da Saudiyya
August 11, 2025Shugaban Ukraine, Volodmyr Zelensky ya yi wasu mabambantar ganawa ta waya da Shugabanin Indiya da Saudiyya a wannan a wani mataki na samun goyon bayansu ga gwamnatin Kyiv, gabanin ganawar Shugaban Rasha, Vladmir Putin da takwaransa na Amurka, Donald Trump. A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Shugaba Zelensky ya ce, ganawa tsakaninsa Firanministan Indiya, Narendra Modi da kuma Yarima mai jiran gado na Saudiya, Muhammad bin Salman ta zo a daidai kuma za su ci gaba da tuntubar juna.
Karin bayani: Trump zai gana da Putin a Amurka
A tattauwarsa da Modi, Shugaba Zelenky ya kara da cewa sun tauna kan sanya takunkumi a kan man Rasha. Zelensky ya kuma kara da cewa, ya tattauna da su kan karfafa matsayarsu a kan Ukraine kan tattaunawar zaman lafiya. Indiya dai na zama babbar mai siyan mai daga Rasha yayin da Saudiyya ke taka rawar mai shiga tsakani a yakin Ukraine.