SiyasaArewacin Amurka
Shugaba Trump ya soke izinin 'dan kasa ga dubban Amurkawa
March 22, 2025Talla
Shugaban Amurka Donald Trump ya soke izinin zama 'dan kasa ga mutane dubu dari biyar da talati da biyu, tare da ba su wa'adin makonni su fice daga kasar.
Karin bayani:Martanin Afirka ta Kudu kan korar jakadanta na Amurka
Mutanen da wannan matakin kora ya shafa sun fito ne daga kasashen Cuba da Haiti da Nicaragua da kuma Venezuela, wadanda suka shiga Amurka a cikin shekarar 2022, karkashin wani tsari da tsohon shugaban kasar Joe Biden ya amince da shi.
Karin bayani:Shugaban Amurka ya rushe wasu hukumomi har da VOA
Wannan dai na daga cikin kudurorin da Mr Trump ya sha alwashin cimma wa a lokacin yakin neman zaben sake koma wa kan karagar mulkin kasar a zango na biyu, bayan fara shi tun a zangon mulkinsa na farko.