Trump ya kuduri aniyar binne ma'aikatar ilimi ta Amurka
March 21, 2025A yayin wani biki da aka shirya a fadar mulki ta White House a ranar Alhamis, shugaba Donald Trump ya saka hannu a kan dokar soke ma'aikatar ilimi ta Amurka, sai dai dokar ba za ta fara aiki gadan-gadan ba har sai ta samu sahalewar 'yan majalisar dokoki.
A lokacin da yake rattaba hannu kan dokar, shugaba Trump ya ce yana fatan ministar ilimi ta yanzu Linda McMahon za ta zama ta karshe a Amurka domin rufe wannan sashe da ya dade yana nuna rashin amfaninsa.
Tun ma kafin rattaba wannan doka dai ministar ilimin ta Amurka Linda McMahon ta soke guraben aiki fiye da 2,000, kusan rababin adadin ma'akaitan da ke aiki a wannan fanni.
Tuni ma dai wasu sanatoci na jam'iyyar Republican inda suka karfafa gwiwa ga matakin na Trump, tare da daukar alwashin ba da gudummowa don dokar ta tsallake karatun majalisa.