Shugaba Trump ya dakatar da kamen bakin-haure a wasu wurare
June 14, 2025Shugaba Donald Trump na Amurka ya umarci jami'an hukumar kula da shige-da-ficen-kasar da su dakatar da aikin samamen kama bakin-haure 'yan ci-rani, a gonaki da otal-otal da ma gidajen sayar da abinci na fadin kasar.
Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito ma'aikatar tsaron cikin gida na tabbatar da samun umarnin, wanda aka mika shi ga hukumar kula da shige-da-fice da kuma ta yaki da fasa-kwauri, to sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters bai kai ga tabbatar da sahihancin umarnin ba.
Tun a lokacin yakin neman zaben shugabancin Amurka zango na biyu Mr Trump ya alkawarta korar bakin-hauren da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba.
Karin bayani:Shugaba Trump da mai dakinsa sun sha ihu a wurin taro
To sai dai wannan mataki ya fuskanci kakkausan suka sakamakon yadda ake kame mutanen da ba su taba aikata laifin komai ba, musamman wadanda ke aiki a gonaki da sauran wurare, lamarin da ya janyo barkewar zanga-zanga a wasu sassan kasar.