Shugaba Trump na Amurka ya gargadi Iran kan yaki da Isra'ila
June 15, 2025Shugaba Donald Trump na Amurka ya gargadi Iran da kada ta kuskura ta kai mata hari ta ko wace fuska, idan ko ta yi gangancin aikata kuskuren, za ta gamu da azabar karfin ikon Amurka mai matukar radadin da ba a taba gani ba.
Jan kunnen na Mr Trump, wanda ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na Truth Social da sanyin safiyar Lahadi, na zuwa ne bayan barkewar yaki mafi muni da aka taba gani tsakanin Isra'ila da Iran da ke tsananin gaba da juna.
Shugaban ya kara da cewa zai iya kokartawa wajen sulhunta kasashen biyu, don kawo karshen wannan rikici da ya janyo asarar rayuka da dama da dukiyoyi.
Matatun man fetur din Iran na ci gaba da aikin hako wa da kuma tace 'danyen man ba tare da fuskantar wani cikas ba, duk kuwa da hare-haren da Isra'ila ta kai wa babbar matatar man Iran ta birnin Tehran cikin dare.
Isra'ila ta sanar da kakkabo jirage marasa matuka da Iran ta kai mata hari da su ranar Lahadi, ko da yake babu karin bayanin yankin da ta harbo su, yayin da kasashen biyu ke ci gaba da kai wa juna hare-hare ba kakkauta wa.
Isra'ila ta ce ta gano gawarwakin wasu mutane biyu da harin Iran ya halaka, wato mutane 10 kenan suka mutu bayan fara yakin.
A wani labarin kuma Isra'ila ta ce an kashe sojanta daya a yankin Gaza na Falasdinu.
Su ko 'yan tawayen Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran, sun sanar da kai wa Isra'ila hare-hare da makamai masu linzami guda 24, a matsayin ramuwar gayyar hare-haren da ta ke ci gaba da kai wa yankin Zirin Gaza na Falasdinu.
Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito cewa harin 'yan tawayen ya sauka a birnin Jaffa, mai tashohin jiragen ruwa da ke tsakiyar babban birnin Tel-Aviv.
To sai dai Isra'ila ta samu nasarar harbo yawancin makaman, wadanda aka kai harin da su cikin sa'o'i 24 da suka gabata, in ji Reuters.
Kungiyar kasashe mafiya karfin tattalin arziki ta duniya G7 na shirin gudanar da taronta na ranar Lahadi a kasar Canada, a daidai lokacin da rikicin Gabas ta Tsakiya ya rincabe, baya ga yakin kasuwancin da shugaban Amurka Donald Trump ya shiga yi da wasu mambobin kungiyar da aminansu.
A jawabin da ya gabatar a kan hanyarsa ta sauka a Canada, firaministan Burtaniya Keir Starmer, ya ce tuni ya tattauna da shugaba Trump na Amurka da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, kan hanyoyin dakatar da yakin, har ma ya tuntubi wasu shugabannin duniya kan lamarin.
Ya kara da cewa sun jima cikin damuwa, game da shirin Iran na samar da makamin kare-dangi na nukiliya, kuma Burtaniya za ta aike da dakarunta zuwa Gabas ta Tsakiya, don ganin yakin bai fantsama ba.
Kasashen da ke cikin kungiyar G7 sun kunshi Canada da Faransa da Jamus da Italiya, sai Japan da Burtaniya da kuma Amurka.