Shugaba Putin ya na 'wasa da wuta' -Trump
May 27, 2025Shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi takwaransa na Rasha Vladimir Putin, inda ya ce ya na wasa da wuta, lamarin da ya zama wani sabon takun saka tsakanin shugabannin biyu, bayan rugujewar tattaunawar samar da zaman lafiya da kasar Ukraine.
Kalaman shugaba Trump da suka gabata a kan Putin ma dai ba su yi wa fadar Kremlin dadi ba, inda shugaban na Amurka ya ce bai san me ya shiga kan Putin ba biyo bayan luguden wuta da Rashar ta yi a kan Ukraine.
Trump zai tattauna da Putin don kawo karshen yaki a Ukraine
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce abin da Putin bai sani ba shi ne da ba don shi ba, da abubuwa marasa kyau da dama sun faru da Rasha.
Ko da yake shugaba Trump bai fadi abubuwa marasa kyau din ba kuma bai yi wata barazana ta kai tsase ga Rasha ko Putin ba a sabbin kalaman nasa.
Trump ya amince da jinkirta karin haraji kan kasashen EU
Har ila yau, ya kuma fada wa manema labarai a ranar Lahadi cewa zai kara lafta wa Rasha takunkumai baya ga wadanda ke kanta a yanzu.