Shugaba Paul Biya zai sake takara
July 14, 2025Shugaba Paul Biya na kasar Kamaru ya sanar a hukumance cewa zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a zaben da ake sa ran gudanarwa cikin watan Oktoba, matakin da ya kawo karshen jita-jitar ko zai sake neman mukamin ko kuma a'a.
Biya ya bayyana hakan ne ta shafinsa na sada zumunta na X, inda ya ce zai tsaya takara a zaben ranar 12 ga Oktoba karkashin jam'iyyarsa ta CPDM, wacce shi ne ke shugabancinta.
Shugaba Biya mai shekaru 92 dai ya shugabanci Kamarun ne tsawon shekaru 43, kuma a ‘yan shekarun nan rashin lafiyarsa ya janyo cece-kuce a cikin kasar.
Wasu daga cikin tsoffin abokan siyasar Biya biyu sun raba gari da shi, kuma a halin yanzu suna neman kujerar shugabancin kasar, ciki har da tsohon Firaminista Bello Bouba Maigari wanda zai tsaya takara a karkashin jam'iyyar UNDP.
Takarar Shugaba Biya ta takwas ke nan a kasar ta Kamaru.