SiyasaJamus
Shugaba Macron ya bukaci daukar matakai a kan Putin
April 6, 2025Talla
Macron ya ce mudin shugaban na Rasha ya ki amincewa da kiran kawo karshen luguden wuta da yake yi a Ukraine dole su dauki mataki.
Wanna kiran dai na zuwa ne bayan wani mumunan hari da sojojin Rasha suka kai a mahaifar shugaban Ukraine Volodmyr Zelensky wanda ya yi sanadiyar rayukar kananan yara tara tare da jikkata wasu da dama.
A baya-bayan nan Faransa da Burtaniya sun gudanar da taruruka don tattauna batun yakin na Rasha da Ukraine da ma na ci gaba da tallafinsu ga kasar ta Ukraine.
Sama da shekaru uku da aka kwashe ana gwabza kazamin fada a tsakanin kasashen dake makwabtaka da juna wanda rikicin ya tagayyara al'ummar Ukraine.
Karin Bayani:Putin ya ba da shawarar Ukraine ta dawo karkashin MDD