A cikin shirin za a ji cewar takkadama ta barke tsakanin kasahen Afirka a zaben wakilan kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dake gudana a yau a birnin New York na Amirka inda ake yin jayaya tsakanin kenya da Djibouti a kan kujera daya, a yayinda yau take ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yaki da gurgusowar hamada.