Kaduna: Shirye-shiryen bikin Easter
April 17, 2025'Yan gudun hijirar dai na shirye-shiryen bikin Easter din cikin kuncin rayuwa, musamman matan da suka rasa mazajensu da marayu da tsofaffi da ke tsugune suna neman tallafi. Wata uwa da ba ta san a fadi sunanta ta bayyana cewa, babu wani shirin da suka yi a wannan bikin na Easter da ke tafe domin ba abun da suka tanadar wa kansu sakamakon yanayin tsadar rayuwa. Ta kara da cewa, a baya ita fitatciyar manomiya ce da ta kware a noman zamani, inda take ciyar da kanta da sauran iyalanta. Mallam Adam Sule dan gudun hijira ne da kuma ke lura da wani sansanin 'yan gudun hijira a Kaduna cikin karamar hukumar Chikum ya ce, babban abin da suke so shi ne komawa garuruwansu na asali domin ci gaba da harkar noman rani da damuna su samu kudin ciyar da kansu da 'ya'yansu. Tuni dai sarakunan garuruwan da 'yan gudun hijirar ke zaune kamar Sarkin Kudansa Maraba Rido a Kaduna Mallam Auta Alkali ke janyo hankalin gwamnati da ta hanzarta bullo da hanyoyin magance wannan fitina, domin samun damar komawar wadannan mutane zuwa garuruwansu na asali.