Shirin zaɓen majalisun dokoki a Rasha
December 3, 2011Mataimakin Shugaban jamiyar CDU CSU a nan Jamus Andreas Schockenhoff yace babu wani sauyi da za a samu game da yada ake gudanar da zaɓe a ƙasar Rasha. Tuni wakilin gwamnatin Jamus akan ƙasar ta Rasha ya soki matakan da mahukuntan ƙasar ke ɗauka akan ƙungiyar Golos mai zaman kanta dake sa ido akan zaɓe . Kimanin mutane miliyan 110 ne za su kaɗa ƙuriunsu a zaɓen majalisar dokkin da zai gudana a gobe lahadi wanda tuni aka tabbatar cewa jamiyar United Party dake mulkin ƙasar ce za ta lashe shi da gagarumin rinjaye. To sai da sakamakon wata ƙuriar jin ra'ayi da aka gudanar ya yi hasahen cewa jamiyar za ta yi hasarar rinjaye na kashi biyu bisa uku da take da shi a majalisa . An dai hana jamiyun adawa masu neman sauyi tsayawa takarar zaɓen . Zaɓen na majalisar Duma dai ana kallon shi ne a matsayin matakin farko na zaɓen shugaban ƙasa da zai gudana a shekara mai zuwa inda za a yi musayar muƙamai tsakanin shugaba Putin da Fraiminista Dmitri Medvedev.
Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala