A cikin shirin za a ji cewa, shugabannin gwamnatocin kasashe da manyan kamfanoni na duniya suna cikin wadanda suke halartar taron tattalin arziki na duniya na shekara-shekara da aka buda a birnin Davos. 'Yan bindiga a kudancin Najeriya, sun fara sabon salon kamfe na hana gudanar da zabukan 2023 a yankin.