Tsohon shugaban gwamnatin mulkin sojan kasar Guinea na kama karya, Moussa Dadis Camara ya musanta zargin hannu kan kisan gillar da aka yi wa masu zanga-zanga tare da fyade wa mata a shekara ta 2009 a birnin Conakry fadar gwamnatin kasar lokacin da yake rike da madafun iko.