A cikin shirin za a ji cewa, dalibai sun fara gudanar da zanga-zanga a tarayyar Najeriya don nuna kosawarsu da yajin aikin da malaman jami'o'i ke yi a kasar. Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da miliyoyin 'yan Najeriya ke fuskantar hauhawar farashin kayayyaki mafi muni cikin shekaru 20.