A cikin shirin akwai rahoto a kan cece-kuce game da wata sabuwar dokar tatsar bayanan jama'a a Nijar da rahoto a kan fatawar cibiyar Al-Azhar a kan cewa Musulmi za su iya sallar idi a cikin gidajensu da rahoto a kan wanda ya yi ridda daga addinin musulumci. Akwai rahoto a kan shirye-shiryen zaben Burundi.