A cikin shirin za a ji cewa Najeriya na ci gaba da yin dari-dari wajen bayar da hadin kanta ga shirin samar da kudin bai daya na ECO tsakanin kasashen ECOWAS, a yayin da a Iraki kuma Amirka ce ke ci gaba da aikawa da karin sojoji duk da janyewar masu zanga-zanga daga ofishin jakadancinta.